Ka zo, Ka zo Immanuel
Ka fanshi ‘ya’yan Isra’ila.
Da ka fashe su daga bauta
Ka shirya musu yankin ƙasa ma.
Korus
Murna! Murna! Yi murna, dukanku!
Ga Allahnku, ya zo ya cece ku.
Ka zo, ka zo, Immanuel
Ka kafa sabon Isra’ila
Da muna cikin bautar Shaiɗan,
Amma ka zo, ka tsinke sarƙoƙi.
Korus
Ka zo, ka zo, Immanuel
Ka tara ‘ya’yan Isra’ila
Mu muna zama da shirinmu
Har ran da za ka zo ka ɗauke mu.
Korus